IQNA

Wahabiyawa Na Kokarin Yada Bakar Akidarsu A Brazil

Bangaren siyasa da zamantakewa; wahabiyawa na yaudarar al'ummar kasar Brazil wadanda bas u da masaniya kan addini a makircinsu na yada maka kuma gurbatacciyar al'adarsu a tsakanin al'ummar wannan kasar musamman ma yadda suke jan hankalin kiristoci a wannan kasa.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wahabiyawa na yaudarar al'ummar kasar Brazil wadanda bas u da masaniya kan addini a makircinsu na yada maka kuma gurbatacciyar al'adarsu a tsakanin al'ummar wannan kasar musamman ma yadda suke jan hankalin kiristoci a wannan kasa. A daidai lokacin guda na yawaitar kiristoci masu karbar musulunci a wannan kasa ta Brazil su kuwa wahabiyawa sun yawaita farfagandar karbar wannan bakar akida a wannan kasa da yawaitar masu karbar akidar wahabiyanci a kasar ta Brazil . Kuma yawancin mutanan daka cikin al'ummar kasar ta Brazil masu karbar wannan akidar na karbar akidar wahabiyuanci a daidai lokacin da suke kokarin shiga da karbar musulunci ba tare da sun banbata akidar wahabiyanci da akidar musulunci ta hakika.


935238