IQNA

Taron Kungiyoyin Jami'oin Musulunci Na Afrika A Sudan

Bangaren siyasa da zamantakewa: a kasar Sudan ne aka gudanar da taron kungiyoyin jami'o'in musulunci na kasashen Afrika da cibiyar bincike da nazarin afrika a jami'ar Khartum fadar mulkin kasar Sudan ta shirya da daukan dawainiyar gudanarwa.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a kasar Sudan ne aka gudanar da taron kungiyoyin jami'o'in musulunci na kasashen Afrika da cibiyar bincike da nazarin afrika a jami'ar Khartum fadar mulkin kasar Sudan ta shirya da daukan dawainiyar gudanarwa.A wajan taron Abdulraham Ahmad Usman shugaban cibiyar bincike da nazarin Afrika a jami'ar Khartum ya bayyana cewa; wannan taron day a samu halartar shugabanni da darektoci da malaman jami'o'in Afrika da wakilan kasashen larabawa a ranar ashirin da biyu ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya har zuwa ashirin da biyar ga watan sun gudanar da taron domin yin nazarin halin da jami'o'in musulunci a kasashen Afrika ke ciki da kuma matsalolin da suke fuskanta da kuma hanyoyin da za su magance su.
934964