IQNA

An Yi Shekara Guda Da Farkawar Musulmi A Tunusiya

14:15 - January 17, 2012
Lambar Labari: 2258621
Bangaren kasa da kasa; bayan sama da shekara guda da kifar da gwamnatin dan kama karya na kasar Tunusiya Zainul Abidina Bin Ali bayan ya bude wuta kan masu zanga zanga da suka tilasta masa yin gudun hijira zuwa kasar Saudiya ,a yau al'ummar musulmin kasar Tunusiya na cimma moriyar yanci na hakika tare da jurewa matsaloli na rayuwa nay au da kullum.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; bayan sama da shekara guda da kifar da gwamnatin dan kama karya na kasar Tunusiya Zainul Abidina Bin Ali bayan ya bude wuta kan masu zanga zanga da suka tilasta masa yin gudun hijira zuwa kasar Saudiya ,a yau al'ummar musulmin kasar Tunusiya na cimma moriyar yanci na hakika tare da jurewa matsaloli na rayuwa nay au da kullum.Dan kma karya na kasar ta Tunusiya ya zubar da jinin fararen hula na kasar da tabka manyan leifuffuka a lokacin da yake rike da madafin ikon kasar da bin manufofin yan mulkin mallaka ido rufe har suka kais hi suka baro shi .Sakamakon farko farko na ra'ayin al'ummar kasar ta Tunusiya da kuma abubuwan da suke rerawa ya yi nuni da yadda suka zabi yanci da tsayawa da gindinsu na kalubalantar duk wani salon a mulkin mallaka bugu da kari suka zabi jam'iyar alnahda mai ra'ayin addinin musulunci karkashin jagorancin Rashid Alganushi da kuma suka mika aakalar musulkin kasar karkashin ikon wannan jam'iya da ta hada guiwa da jam'iyar da ta zo ta uku a zabukan da aka gudanar a kasar.
935318

captcha