Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; mu'assisar kasa da kasa: ta Almahdi ta tatara labaran rayuwa shahidai sha hudu na duniyar musulmi a wani kundi da ta yiwa lakabin Parihaye Fulad kuma wannan kundi ya kumshi rayuwarsu ta gwagwarmaya . A cikin jildi goma sha hudu ne aka halhada rayuwar wadannan shahidai kan rayuwarsu da gwagwarmayarsu kuma wadannan shahidai sune Shaihid Mustapha Camran,Shahid Ahmad Mutawasiliyan,Shadi Kutub,Shahid Yahya Ayashi,Shahid Ahmad Yasin,Shahid Fathi Shakaki,Shahid Said Abas Musawi,Shahid Imad Muniya,Shahid Said Arif Husein Huseini, Shahid Muhammad Bakir Hakim,Shahid Bakir Sadre,Shahid Hasan Albana,Shahid Burhanul Dine Rabbani da kuma Shahid Ahmad Sha Mas'ud kuma za a nuna da watsa wannan littafin day a kumshi rayuwar shahidai a daidai lokacin gudanar da taro na fadakar da musulmi da matasa a duniyar musulunci da za a gudanar a watan Bahman mnai zuwa.
935774