IQNA

Wasu yahudawan Sahyuniya Sun Yi Kira Da A Saki Husni Mubarak

19:10 - January 17, 2012
Lambar Labari: 2258824
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman yahudawan sahyuniya sun yi kira bangaren shari'a na kasar Masar da a saki Husni Mubarak saboda yanayin rashin lafiya da yake ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-qabs cewa, wasu daga cikin malaman yahudawan sahyuniya sun yi kira bangaren shari'a na kasar Masar da a saki Husni Mubarak saboda yanayin rashin lafiya da yake ciki a gidan kurkukun da ake tsare da shi.
Masu zanga-zanga a birnin Tripoli na kasar Libiya sun kutsa cikin hotel din da shugaban mulkin sojin kasar Masar Field Mashal Muhammad Husain Tantawi yake ganawa da manyan jami'an kasar Libiyan don nuna rashin amincewarsu da yadda kasar Masar din ta gaza wajen kama magoya bayan tsohon shugaban kasar Libiyan Kanar Mu'ammar Gaddafi da suke ci gaba da zama a kasar Masar din.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Libiyan sun ce masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne a hotel din dauke da kwalaye da a jikinsu suka rubuta bukatunsu na a kamo tsoffin magoya baya da kuma jami'an tsohuwar gwamnatin da dawo da su gida don fuskantar shari'a.
Har ila yau kuma masu zanga-zangar sun tare hanyoyin da 'yan tawagar shugaban mulkin sojan na Libiyan za su fice daga hotel din bayan barin shugaban hotel din, suna masu Allah wadai da shugabannin sojin kasar Masar din.
Masu zanga-zangar dai suna zargin kasar Masar din da ba da mafaka ga wasu daga cikin jami'an sojin tsohuwar gwamnatin Libiyan bayan da suka gudu daga kasar.
935768


captcha