IQNA

Farkawar Musulmi Imam Khomeini Ya yI Hassashe Kan Makomar Duniya

Bangaren kasa da kasa: tashin baya bayan nan a yankin da musulmi suka yi na tabbatar da tsinkayen da Imam Khomeini Muassashin jamhuriyar musulunci tai ran ya yi kan makomar duniya da kuma fadadar juyin juya halin musulunci na Iran .


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; tashin baya bayan nan a yankin da musulmi suka yi na tabbatar da tsinkayen da Imam Khomeini Muassashin jamhuriyar musulunci tai ran ya yi kan makomar duniya da kuma fadadar juyin juya halin musulunci na Iran .Nada Badram malama a jami'ar musulunci ta kasar labanon a wata tattaunawa da ta hada tad a kamfanin dillacin labarai na Ikana ta yi bayanin cewa; bayan nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a shekara ta dubu daya da dari uku da hamsin da bakwai hijira shamsiya ,imam Khomeini ® ya kwatamta wannan juyin juya halin musulunci a matsayin wanda bai takaita da iyakokin Iran kadai ba a'a zai yadu a fadin duniya kuma wannan tashi da farkawa daga barci na baya bayan nan da musulmin yankin ke yi a hakakanin gaskiya na tabbatar da wannan Magana ta Imam Khoemeini ® a wancan lokaci da kuma yadda na nuni matsayinsa da hangen nesansa.Ta kara da cewa: adalci da kwatamta gaskiya a tsakanin mutane shi ne zai sa a ji dadin mulki.
935208