IQNA

Zaman Lafiya Da Kasantuwar Suriya Tabbaci Ne Ga Yankin Da Na Musulmi

17:42 - January 18, 2012
Lambar Labari: 2259493
Bangaren kasa da kasa: mataimakin shugaban komitin koli na musulmi yan shi'a a kasar Labanon ya jaddada cewa: dole mu kare tsaro da kasantuwar kasar Suriya domin kare kasar Suriya shi ne zai ba mu tabbaci na kasantuwar yankin larabawa da na musulmi da kara ma karfin guiwa da tsaro a tsakaninmu.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; mataimakin shugaban komitin koli na musulmi yan shi'a a kasar Labanon ya jaddada cewa: dole mu kare tsaro da kasantuwar kasar Suriya domin kare kasar Suriya shi ne zai ba mu tabbaci na kasantuwar yankin larabawa da na musulmi da kara ma karfin guiwa da tsaro a tsakaninmu.Ayatullahi Abdul Amir Kablan mataimakin shugaban komitin koli na musulmi yan shi'a a kasar Labanon a daidai lokacin da Ahmad Dawud Uglo ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya kai ziyarar aiki a kasar ta Labanon ya jaddada masa cewa: mu muna adawa da duk wani naui na haddasa fitina na addini ko na kabilanci kuma na fada da duk wata fitina kuma muna kira da hadin kai na al'umma da kabilu da kuma hadin kai a tsakanin musulmi.A yau musulmi na bukatar kalubalantar babban makiyansu Haramtacciyar kasar Isra'ila mai kula wa musulmi makirci kuma dole musulmi su hada kansu domin dagile makirci da ake kulla masu lokaci ne na hadin kai a tsakanin musulmi.
936206
captcha