IQNA

Rushdie Na Ci Gaba Da Tsoron Yiyuwar Zartar Da Fatawar Imam A Kansa

15:39 - January 21, 2012
Lambar Labari: 2260659
Bangaren kasa da kasa:kungiyoyin musulmi na Indiya bayan sun jinjina da godiya ta musamman kan kokarin da musulmi ke yin a ganin sun hana Salman Rushdi ya kai ziyara a kasarsu sun bayyana cewa wannan babban nasara ce ga musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyoyin musulmi na Indiya bayan sun jinjina da godiya ta musamman kan kokarin da musulmi ke yin a ganin sun hana Salman Rushdi ya kai ziyara a kasarsu sun bayyana cewa wannan babban nasara ce ga musulmi.

La'anannen marubucin nan dan kasar Indiya Salman Rushdie ya bayyana cewar ba zai halarci wani bikin marubuta da aka shirya gudanarwa a garin Jaipur na kasar Indiyan ba saboda tsoron cewa wasu za su nemi kashe shi.
Cikin wata wasika da ya aike wa wadanda suka shirya wannan bikin Mr. Rushdie wanda al'ummar musulmi suke nema ruwa a jallo ya ce jami'an tsaro sun shaida masa cewa akwai yiyuwar wasu su zo wajen da niyyar kashe shi, don haka ba zai halarci taron wanda shi ne irin sa mafi girma da ake gudanar a kudancin nahiyar Asiya. Tun farko dai malaman yankin sun nuna rashin amincewarsa da halartarsa wannan taron.
A shekarar 1989 marigayi Imam Khumaini (r.a) ya fitar da fatawar hukumcin kisa a kan Rushdie sakamakon rubuta littafin Ayoyin Shaidan da ya yi inda ya ci mutumcin Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) lamarin da ya sanya shi zama cikin buya tun daga wancan lokacin har zuwa yau din nan.

938304
captcha