Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: gwamnatin Tailand a jiya ashirin da tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta aike da mahukumtan Palasdinu wata wasika da a cikinta a humce suka amince da Palasdinu a matsayin kasa da cin gashin kanta mai cikekken yanci.An nakalto daga kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP cewa: majiyar kusa da ma'aikatar harkokin wajan Palasdinu c eta sanar da cewa: gwamnatin kasar Tailand ta aike da wani sako mai muhimmanci da a ciki ta amince da yankin da aka shata a shekara ta dubu daya da dari tara da satin da bakwai miladiya a matsayin kasar Palsdinu mai cikekken yanci.Riyad Almali ministan harkokin wajan yankin Palasdinu mai cin kwarya kwaryar yanci ya jaddada cewa; Tailand it ace kasa ta farko a wannan sabuwar shekara ta dubu biyu das ha biyu da ta amince da Palsdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
938285