IQNA

Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Halartar Larabawa A Taron Yahudawan Sahyuniya

20:58 - January 26, 2012
Lambar Labari: 2262665
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka a yankin.
940425

captcha