IQNA

Khalid Mush’al Ya Gana Da Babban malamin Jmai’ar Azhar A Birnin Alkahira

20:58 - January 26, 2012
Lambar Labari: 2262673
Bangaren kasa da kasa, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar palastinu Khalid Mus’al ya gana da babban malamin jami’ar Azahar da ke birnin Alkahira na kasar Masar dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar palastinu Khalid Mus’al ya gana da babban malamin jami’ar Azahar da ke birnin Alkahira na kasar Masar dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin baki daya musamman ma a yankin gabas ta tsakiya.
An gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia tare da halartar dubban daruruwan mutane da suka gudanar da zanga-zangar goyion baya ga juyi da kuma yin Allawadai da halaratr sarkin Qatar a wurin wadannan taruka.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki Qatar a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar.
Dubban masu zanga-zanga a birnin Saqas na kasar Tunisa, sun daga kyallaye da kwallaye da aka rubuta cewa, sarki Qatar Karen farautar Amurka da yahudawa ne, saboda haka al'ummar Tunisia ba su lalae marhabin da shi a kasarsu.
940381


captcha