Kmafanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na actualitie.fr cewa, jam’iyar adala wal hurriya ta kungiyar Ikhwan a kasar Masar wadda ta lashe zaben kasar ta ce ba za ta sanar da sunan takarar neman shugabancin kasar ba dag acikin jam’iyar amma dai za a ji matsayinta dangane da wannan batu sai nan gaba kamar yadda kakakkin jam’iyar ya sanar a yau.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi. 941321