IQNA

Wajibi Musulmi Su Yi Takatsantsan da makiyansu

Bangaren siyasa : musulmi masu rayuwa a tsakiyar wadanda ba musulmi bad a kuma musulmi da ke rayuwa a kasashen musulmi da masu ra'ayin juyin juya halin musulunci ya zama wajibi a yau su fahimta da sanin makiyansu da kuma fahimtar irin makircin da makiyansu ke kulla masu a yau.


Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; musulmi masu rayuwa a tsakiyar wadanda ba musulmi bad a kuma musulmi da ke rayuwa a kasashen musulmi da masu ra'ayin juyin juya halin musulunci ya zama wajibi a yau su fahimta da sanin makiyansu da kuma fahimtar irin makircin da makiyansu ke kulla masu a yau.A wannan rayuwa ta yau komi ya fito fili karara kan yadda makiya musulmi ke kullawa musulmi makirci da zgon kasa ta fuskoki da dama kuma daban daban .Idan aka yi la'akari da nasarorin da musulmi suka samu da kuma suke ci gaba da samu a yau da kuma wadanda suka gabata a tsawon tarihin musulunci za a iya fahimtar muni da karfin makircin da makiya musulmi ke kullawa musuluni da addaininsu kuma lokaci ya yi day a kamata musulmi da shugabanninsu da kungiyoyin musulmi a kasashen musulmi da kuma duk inda musulmi suke na fuskantar wannan matsala da magance ta wato kawo karshen makircin da makiya musulmi ke kulla masu.
941543