Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka tare da halartar manyan malaman addinin muslunci na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na fratman cewa, ana shirin fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka tare da halartar manyan malaman addinin muslunci na kasar kamar dai yadda aka saba gudanarwa akowace shekara a birnin Abijan fadar mulki.
Bayanin ya ci gaba da cewa babban kwamitin malaman addinin addinin muslunci da limaman masalatai ta kasar Ivory Coast ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro na murnan zagayowar lokacin haihuwar manzon Allah (SAW) wanda dukaknin musulmi suke girmamawa a ko’ina cikin fadin duniya baki daya.
Yanzu haka dai ana shirin fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka tare da halartar manyan malaman addinin muslunci na kasar ta Ivory Coast, wadda daya ce daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka mai matukar muhimmanci.
942608