Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa, al’ummar kasar Bahrain sun ambaci wannan mako da suna makon yin tsayin daka a gaban azzaluman sarakunan kasar Bahrain da suke yin amfani da dukkanin karfinsu wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar da kuma hakkokinsu na ‘yan kasa da aka harmta musu.
A banagare guda kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabaci.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar ta Saudiyya.
Tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
942655