IQNA

Farkawar Al’ummar Musulmi Ba Ta San Sunna Ko Shi’a Ba

21:57 - January 31, 2012
Lambar Labari: 2266016
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa fadakar al’ummar musulmi ba ta san wani abu shi’a ko sunna ba, domin farkawa ce ta mabiya dukaknin mazhabobin muslunci baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfin jagoran juyin juya halin muslunci a Iran cewa, a safiyar litinin ne jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan matasa da suka fito daga kasashe 73 na duniya mahalarta taron kasa da kasa na matasa da farkawa ta Musulunci da ake gudanarwa a birnin Tehran.
A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yunkurin al'ummomin kasashen musulmi na kifar da shugabannin kama-karya ‘yan amshin shatan manyan kasashen duniya a matsayin lamari mai matukar muhimmanci sannan kuma wani mafari na yunkurin ganin bayan lalatattun cibiyoyin yahudawan sahyoniya da ma'abota girman kan duniya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sakamakon wannan yunkuri mai cike da albarka, da yardar Allah al'ummar musulmi za su sake dawo da daukaka, ‘yanci da kuma tsayin dakan da suke shi a baya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana matasan kasashen musulmin a matsayin masu dauke da babbar bishara ga makomar al'ummar musulmi, daga nan sai ya ce: Farkawar da matasan kasashen musulmi suka yi, lamari ne da ke kara irin fatan da ake da shi na farkawar dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu tarihin bil'adama yana fuskantar wani gagarumin sauyi mai girma ne, daga nan sai ya ce: Bil'adama dai sun gwada dukkanin akidu na abin duniya da suka hada da gurguzu, jari hujja, ‘yan kasanci da rashin yarda da Ubangiji, to amma a halin yanzu suna a wani sabon yanayi ne wanda babbar alamar hakan ita ce irin yadda al'ummomi suka koma ga Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimako daga wajen karfi maras karewa na Ubangiji da kuma dogaro da koyarwar Ubangiji.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin yadda gungun ‘yan kama karya da kuma lalatattun yahudawan sahyoniya da sauran ma'abota girman kan duniya suke juya duniya yadda suke so, Jagoran cewa ya yi: Yunkurin al'ummomin wannan yankin wajen tinkarar lalatattun ‘yan kama-karya wani bangare ne na gwagwarmayar bil'adama da mulkin kama-karyar yahudawan sahyoniya, sannan kuma bayan wani yanayi mai girma na tarihi, bil'adama za su tsira da wannan kama-karya mai tsananin hatsari. Ko shakka babu wannan sauyi mai girma da ke faruwa tabbaci ne na alkawarin Ubangiji na ‘yantar da al'ummomi (daga mulkin ‘yan kama-karya) da kuma tabbatar da iko na koyarwar Ubangiji.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan irin mutanen da suke ganin ba za a iya samun nasara a kan wadannan cibiyoyin kama-karya na yahudawan sahyoniya na duniya ba, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A shekarun baya da dama ba su yarda da cewa muminan matasan kungiyar Hizbullah (ta kasar Labanon) za su iya samun nasara a kan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ko kuma yiyuwar faduwar dagutun kasar Masar (Hosni Mubarak) da kuma gagarumin sauyi mai ban mamaki da aka samu a kasashen arewacin Afirka ba, haka nan irin tsayin daka, nasarori da kuma ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta samu. To amma gagarumin karfi na Ubangiji ya bayyanar da kansa cikin irin wadannan nasarori da kuma sauyi mai ban mamaki da ya faru.
Ayatullah Khamenei ya bayyana kasantuwar al'ummomi a fage a matsayin share fagen cimma irin wannan taimako na Ubangiji daga nan sai ya ce: Sakamakon tabbatar wannan alkawari na Ubangiji ne a halin yanzu yahudawan sahyoniya, babbar shaidaniya Amurka da sauran masu takama da karfi na kasashen yammaci suka gaza wajen tinkarar wannan farkawa ta Musulunci da ake ci gaba da samu. Sannan kuma a kowace rana irin wannan rauni da gazawar da suka yi sai karuwa suke yi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin sauyin da ake samu a kasashen musulmi a matsayin wani mafari kuma share fagen tafarkin ‘yanci da sa'ada. Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da yake da muhimmanci shi ne cewa bai kamata mu dauki irin wadannan nasarori da aka samu a matsayin karshen tafiyar da muke yi ba. Wajibi ne mu ci gaba da gwagwarmaya da masu takama da karfi na duniya ta hanyar tsayin daka da dogaro da irada ta al'ummomi da kuma kyautata zato ga Allah Madaukakin Sarki.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin nasarorin da Jamhuriyar Musulunci take ci gaba da samu a fagen ilimi musamman fasahar nukiliya, likitanci da sauran su, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Muminan matasan kasar nan sun sami irin wadannan nasarorin da suka samu ne duk kuwa da irin makirci da kafar ungulun makiya, wanda hakan yana iya zama abin koyi ga dukkanin matasan kasashen musulmi.
Ayatullah Khamenei ya yi karin haske dangane da kokarin da makiya suke yi na sanya wasu munanan tunani da ke cike da kuskure cikin zukatan al'ummar musulmi inda ya ce: Kimanin karnoni biyu kenan makiyan al'ummar musulmi suka ciyar da al'ummar musulmi baya ta hanyar sanya musu jin cewa su masu rauni ne da kuma cewa babu yadda za a iya yin nasara a kan masu takama da karfi na duniya, to amma a yau kan al'ummar musulmi sun farka sun fahimci cewa dukkanin wadannan tunani guda biyu kuskure ne dari bisa dari sannan kuma al'ummar musulmi suna da karfin sake dawo da irin karfi da kuma ci gaban da duniyar musulmi take da su.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan karnin da ake ciki a matsayin Musulunci da kuma riko da koyarwar Ubangiji.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da ma'abota girman kai suke yi wajen cike gurbin irin rashin nasarar da suka fuskanta sakamakon wadannan yunkuri na al'ummomi a kasashen Masar, Tunusiya da Libiya da sauran kasashen musulmi, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A halin yanzu dai makiya suna ta shirye-shirye da kulla makirci ne. Don haka wajibi ne al'ummomin musulmi musamman matasan cikin su wadanda su ne tushen wannan farkawa ta Musulunci su yi taka tsantsan da kumaamfani da irin kwarewar sauran al'ummomi wajen ganin ba su kwace musu wannan juyi na su da kuma kautar da su daga tafarkin da suke kai ba.
Jagoran ya yi ishara da irin kwarewa ta shekaru 32 da Jamhuriyar Musulunci take da ita wajen tinkarar makirce-makircen Amurka da sauran makiya Musulunci daga nan sai ya ce: Ma'abota girman kan duniya dai sun yi amfani da duk wani karfi da kuma dama da suke da ita wajen kawar da Jamhuriyar Musulunci, to amma ya zuwa yanzu dai sun sha kashi a gaban al'ummar Iran a dukkanin fagage, a nan gaba ma za su ci gaba da fuskantar irin wannan rashin nasarar da shan kashin ne.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar haifar da rarrabuwa a tsakanin al'ummar musulmi a matsayin daya daga cikin makirce-makircen makiyan yana mai cewa: Babu ruwan yunkurin farkawa ta Musulunci da batun Shi'a da Sunna, a halin yanzu dai dukkanin mabiya mazhabobi daban-daban na Musulunci, cikin hadin kai da kaunar juna, ne suke a fagen wannan gwagwarmayar.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da ababen da al'ummar musulmi suka yi tarayya cikinsu kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Akwai bambanci tsakanin al'ummomin musulmi a tsakaninsu bisa la'akari da yanayi na waje da kuma tarihi da sauransu, to amma duk da hakan abin da yake da muhimmanci shi ne dukkanin su suna adawa da iko na na shaidanci na yahudawan sahyoniya da kuma Amurka, kamar yadda kuma ba su amince da kasantuwar wannan cutar kansa mai suna Isra'ila ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Wajibi ne a yi taka tsantsan kan duk wani abin da aka gani wanda zai amfani Isra'ila da Amurka, sannan kuma mu dauki hakan a matsayin wani yunkuri na makiya wanda ba zai amfani al'ummomin mu ba. Sannan kuma a duk inda aka ga wani yunkuri na adawa da sahyoniyanci da girman kan duniya da mulkin kama-karya da yada fasadi, to kuwa al'ummar musulmi za su goyi bayan hakan da dukkan karfinsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yunkurin mayar da yunkurin al'ummar Bahrain a matsayin saniyar ware a matsayin daya daga cikin kokari da kuma makircin da ma'abota girman kan duniya suke yi ta hanyar kafafen watsa labaransu yana mai cewa: a kokarin da kafafen watsa labaran kasashen yammaci ko kuma wadanda suke da alaka da su suke yi wajen haifar da rarrabuwan kai da kuma dushe hasken wannan yunkurin shi ne bayyana yunkurin al'ummar Bahrain a matsayin wani rikici tsakanin Shi'a da Sunna. To amma babu wani bambanci cikin wadannan yunkuri na farkawa ta Musulunci da ke faruwa a kasashe daban-daban.
Ayatullah Khamenei ya bayyana dogaro da Allah da kuma kiyaye hadin kai a matsayin alama ta nasara, sannan kuma yayin da ya ke ishara da umurnin da Allah Madaukakin Sarki ya ba wa Manzonsa (s.a.w.a) na yin tsayin daka, cewa ya yi: ko shakka babu al'ummar musulmi ta hanyar riko da wannan umurni na Ubangiji za su ci gaba da tafiya a kan wannan tafarkin da suka rika.
Daga karshe dai Jagoran ya bayyana irin fata mai kyau da yake da shi dangane da duniyar musulmi inda kuma ya kirayi al'ummomin kasashen musulmi da su kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu.
Tun da farko dai sai da babban sakataren majalisar kasa da kasa ta farkawa ta Musulunci Dakta Ali Akbar Wilayati ya gabatar da jawabinsa inda yayin da ya bayyana cewar wannan taron dai ya kumshi kimanin matasa 1200 ne da suka fito daga kasashe 73 na duniya. Dakta Wilayati ya ci gaba da cewa: An kasa mahalarta taron ne zuwa kwamitoci guda shida inda za su tattauna kan maudhu'ai da suka hada da: "Tushe na nazari da tunani da kuma abubuwan da za su ciyar da farkawa da Musulunci gaba" "Iko na Musulunci, ababen koyi, nasarorin da aka samu da kuma matasa" "Girman kan duniya, Amurka da yahudawan sahyoniya wajen tinkarar wannan yunkuri na farkawa ta Musulunci", "Matasa, gwagwarmayar Palastinu da kuma farkawa ta Musulunci", "Gano irin dama da kuma abubuwan da suke barazana ga farkawa ta Musulunci" sai kuma "Makomar farkawa ta Musulunci".
Har ila yau kuma Dakta Wilayatin ya yi karin haske dangane da wajibcin fada da makirce-makircen ma'abota girman kan duniya musamman ma irin kararrakin da suke yadawa ta kafafen watsa labaransu a kokarin da suke yi wajen ganin bayan wannan yunkuri da kuma farkawa ta Musulunci.
Har ila yau kuma wasu daga cikin matasan su ma sun gabatar da jawabai inda suka bayyana mahangarsu kan wannan batu.
943679


captcha