IQNA

An Bude Ofishin Jigilar Musulmi A Jamus

16:25 - February 02, 2012
Lambar Labari: 2267127
Bangaren kasa da kasa: a birnin Barlin na kasar Jamus da ke nahiyar turai an kaddamar da wani shiri mai matukar muhimmanci da zai rika yin jigilar musulmi da aka bawa sunan Taxin Musulmai da wani dan asalin kasar Iraki da ke zaune a birnin na Barlin ya kafa.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: a birnin Barlin na kasar Jamus da ke nahiyar turai an kaddamar da wani shiri mai matukar muhimmanci da zai rika yin jigilar musulmi da aka bawa sunan Taxin Musulmai da wani dan asalin kasar Iraki da ke zaune a birnin na Barlin ya kafa.Salim Ra'id wani musulmi dan kasar Iraki ne da ke zaune a wannan kasa ta jamus ya kafa wani taxi da za ta rika jigilar musulmi da ke zaune a wannan kasa ta jamus da ke nahiyar turai kuma ko ba komi za ta taimaka matuka gaya wajan warware da kuma rage matsalar da musulmi ke fuskanta ta fuskar jigilarsu a wannan kasa.Kuma musulmi da dama ne suka ji dadi da kuma farancikin jin dadin wannan tsari da mataki na bawa musulmi wannan dama ta yin jigilarsu da kuma shiga cikin motocin cikin tsari da kuma shiga ta musulunci.

944899
captcha