IQNA

Babban Burin Yahudawan Sahyuniya Shi Ne Haramta Ma Palaetiwa Hakkokinsu

21:07 - February 02, 2012
Lambar Labari: 2267208
Bangaren kasa da kasa, jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar manufar yahudawan sahyuniya ita ce su ga sun raba al’ummar palastine da dukkanin hakkokinsu tare da mayar da su ‘yan gudun hijira baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabjin din Almanar cewa, jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar manufar yahudawan sahyuniya ita ce su ga sun raba al’ummar palastine da dukkanin hakkokinsu tare da mayar da su ‘yan gudun hijira baki daya kamar dai yadda ake gani a halin yanzu.
Babbar kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan, kmar yadda kuma kasashen larabawa da suke babatun kare hakkokin palastinawa suka gum da bakunansu kan wannan batu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na CPI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
945107


captcha