Bangaren kasa da kasa: masu nuna adawarsu da bakar siyasar kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa a yankin Zirin Gaza sun tarbi motar da ke dauke da babban sakataren majalisar dinkin duniya da takalma da duwatsu domin nuna masa adawarsu da fushinsu kan bakar siyasa da siyasar harshen damo da suke nunawa al'ummar palsadinu.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: masu nuna adawarsu da bakar siyasar kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa a yankin Zirin Gaza sun tarbi motar da ke dauke da babban sakataren majalisar dinkin duniya da takalma da duwatsu domin nuna masa adawarsu da fushinsu kan bakar siyasa da siyasar harshen damo da suke nunawa al'ummar palsadinu. Yawancin mutanan da suka yi wa babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Mon wannan gagaramar tarba da takalma da duwatsu yawancinsu iyalan shahidai da manoma da iyalan maras lafiya a yankin na Zirin Gaza suka yi masa wannan tarba suna nuna adawarsu dab akin cikinsu da yadda majalisar dinkin duniya da hukumomi na kasa da kasa ke nuna masu wari da banbanci da yi wa lamarinsu rikon sakainar kasha.
946251