IQNA

Mabiya Addinin Muslunci A Kasar China Sun Gudanar Da Tarukan Maulidi

17:37 - February 05, 2012
Lambar Labari: 2269027
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin musulunci a kasa China sun gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a garuruwa daban-daban inda aka cika masallatai da kuma cibiyoyin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun cewa, mabiya addinin musulunci a kasa China sun gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a garuruwa daban-daban inda aka cika masallatai da kuma cibiyoyin addini da suke cikin kasar ta China.
A bangare guda kuma A daidai lokacin da kasashen Yamma da kuma wasu kasashen Larabawa suke cike da kwarin gwiwar samun goyon Kwamitin Tsaro na MDD kan yiyuwar amincewa da kudirin da zai yi Allah wadai da gwamnatin Siriya, ko a jiya asabar kasashen Rasha da China sun sa kafa sun yi fatali da wani sabon daftari da aka gabatar kan wannan batu ta hanyar hawan kujerar naki.
Wannan dai shi ne karo na biyu da kasashen na Rasha da China ke yin amfani da matsayinsu a kwamitin na tsaro domin nuna adawarsu da kudurin na kasashen Turai da Amurka da kuma wasu kasashen larabawa da ke neman a la'ancin gwamnatin Basharul Assad bisa zargin cewa tana kashe fararen hula. Sakamakon rashin samun nasara a wannan zama da aka gudanar a yammacin jiya, kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Faransa wanda su ma ke da matsayin masu kujerar naki a Majalisar, sun zargi Rasha da China da rufe ido a daidai lokacin da ake ci gaba da zubar da jinin al'umma a kasar ta Syria.
To sai dai tun kafin kwamitin na tsaro ya yi zamansa ne ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya bayyana cewa ko a wannan karo kasarsa ba za ta amince da kudurin ba saboda kasancewarsa mai nuna bangaranci da kuma rufe ido a kan gaskiya. Lavrov ya ce warware rikici irin wanda ke faruwa a kasar Syriya ba ya bukatar shisshigi, domin kuwa wannan rikicin cikin gida ne wanda ake iya warware shi ta hanyar tattauna a tsakananin bangarorin da ya shafa.
A can baya dai kasar Rasha ta yi iya kokarinta domin ganin cewa 'yan adawa da kuma gwamnatin Sriya sun halarci wata tattaunawar sulhu a birnin Moscou domin warware wannan rikici, tattaunawar da 'yan adawar masu samun goyon bayan Amurka da kuma wasu sarakunan Larabawa suka ce ba za su taba halarta ba.
946640

captcha