IQNA

Ci Gaba Da Yin Suka A Kan Shirin Yahudantar Da Qods A Kasashen Musulmi

17:36 - February 05, 2012
Lambar Labari: 2269028
Bnagaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci da ma sauran al’ummomi masu lamiri a duniya suna ci gaba da yin suka da kakkausar murya kan yadda yahudawan sahyuniya suke ci gaba da cin karensu abbu babbaka a kan masallacin Qods da sauran wurare masu alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikion jagororin kungiyar Amal ta kasar Lebanon Hassan Qabalan ya sheda cewa, mabiya addinin muslunci da ma sauran al’ummomi masu lamiri a duniya suna ci gaba da yin suka da kakkausar murya kan yadda yahudawan sahyuniya suke ci gaba da cin karensu abbu babbaka a kan masallacin Qods da sauran wurare masu alfarma da suke cikin birnin mai albarka, da ma sauran wurare da suke cikin yankin palastinu, da kumahankoron haramtacciyar kasar Isra’ila na yahudantar da Birnin.
Jim kadan bayan jefa kuri'a a kwamitin tsaro, jakadan kasar rasha a Majalisar ta dinkin duniya Vitaly Churkin, ya ce abin da kasarsa ta yi, ta yi hakan ne domin hana barkewar yakin basasa a Syriya, sannan kuma har gobe kasarsa na mai fatar ganin an warware wannan rikici amma ba ta hanyar samar da kuduri da zai tilasta wa shugaba Basharul Assad damka ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa tare kuma da kafa gwamnatin hadin kasa wacce za ta shirya sabbin zabuka ba.
Ita kuwa kungiyar larabawa wacce take sahun gaba wajen ganin an kawar da Basharul Assad daga kan karagar mulki, duk da rahoton da tawagar 'yan kallon da ta tura zuwa kasar domin su shaidi yadda lamurra ke tafiya a Siriya mai cewa idan har ma sojojin Syria na buda wuta a kan jama'a to lalle kuwa akwai daruruwa jama'a da ke dauke da manyan makamai wadanda su ma ke kai wa kadarori da kuma sojojin kasar hari, to amma sakamakon tsayuwar da wasu shuwagabannin Larabwan suka yi na kare muradun kasashen Yamma, hakan ya hana wa kungiyar yin aiki da wannan rahoto, a maimakon hakan ma, sai ta gaggauta janye wannan tawaga daga kasar ta Sirya.
Kwana daya kafin wannan zaman da kwamitin tsaro ya gudanar, shugaban tawagar kungiyar ta larabawa, Janar Mohammad Al-Dabi dan kasar Sudan, ya gabatar da wani taron manema labarai inda ya bayyana cewa wasu shuwagabannin larabawa sun yi ayyukan tawagarsa shisshigi sannan kuma suka sauya ma'anar rahoton da ya gabatar masu.
Babban abin tambaya a nan dai shi ne, ko me ya sa har yanzu ba daya daga cikin kasashen Turai, ko Amurka ko kuma kungiyar ta larabawa da ta taba neman bangarorin da ke da hannu a rikicin na Sirya domin su zauna a kan teburin tattaunawa, inda a maimakon haka suna kokarin kawar da Basharul Assad ne kawai daga kan karagar mulkin kasar ta Syria.
945815


captcha