Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; mai bada shawara kan harkokin kur'ani a hukumar kula da al'adu da dangantaka ta musulunci a jamhuriyar musulunci ta Iran ya bada labarin gudanar da wani mako na karatun Kur'ani mai tsarki a kasashe daban daban a dalilin zagayowar ranar haifuwar fiyayyan halitta ma'aikin Allah Muhammad dan abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma zagayowar kwanaki goma na nasarar juyin juya halin musulunci ta Iran.Ahmad Zarangar mai bada shawara kan karatunkur'ani a hukumar da ke kula da al'adu da dangantaka ta musulunci a wata tattauanwa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikan ya bayyana cewa wannan gasar ta zo a daidai lokaci guda da makon hadin kai da kuma goma ta nasarar juyin juya halin musulunci a Iran da kuma ake gudanar da irin wannan shagula a sauran kasashe na duniya.
945556