IQNA

Tarukan Makon Hadin Kai Da Na Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran

Bangaren al'adu da fasaha; a daidai lokaci guda na gudanar da raya makon hadin kai da kuma fara shagulan tunawa da goma ta nasarar juyin juya halin musulunci tai ran an shirya shagulgula iri-iri masu kayatarwa a ofishin kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasar Serelanka.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokaci guda na gudanar da raya makon hadin kai da kuma fara shagulan tunawa da goma ta nasarar juyin juya halin musulunci tai ran an shirya shagulgula iri-iri masu kayatarwa a ofishin kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasar Serelanka.Daga cikin abubuwan da za a gabatar akwai wakoki na yabon juyin juya halin n=musulunci a Iran da kuma nasarar juyin juya halin da kuma wasu wakokin da suka shafi makon hadin kai a tsakanin musulmi. Har ila yau za a gabatar dajawabai da bahasi kan muhimmancin hadin kai a tsakanin musulmi da kuma yadda ya kamata mausulmi su hada kansu da hanyoyin day a kamata musulmi su bi domin samar da hadin kai a tsakanin musulmi da kuma wasu bayanan kan nasarar juyin juya halin musulunci da kuma yadda aka cimma nasarar a wancan lokaci.

946575