Bangaren siyasa da zamantakewa: a kasar Indiya a yau sha shida ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gudanar da gasar tarihin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkak a garin Delhu No fadar mulkin kasar ta Indiya .
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a kasar Indiya a yau sha shida ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gudanar da gasar tarihin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkak a garin Delhu No fadar mulkin kasar ta Indiya .Wannan gasar an fara ta ne tare da karatun wasu ayoyin kur'ani mai girma da makaranci Manhaj Alabidin daya daga cikin fitattun makaranta kur'ani na birnin ya karanto kana daga bisani malamai dam asana addinin musulunci suka gabatar da jawabi da hudubobin jan hankalin matasa da wadanda suka halarci wannan gasar kan muhimmancin sanin tarihi da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka.
946755