Bangaren kasa da kasa: gwamnatin kasar Maroko a cikin kasa da wata guda na bayan nan sau hudu ken an tana hana buga wasu rubuce-rubucen cin mutumci da Fuska kan abubuwa masu kima da daraja na addinin musulunci da wata jaridar kasar Faransa ta buga da kuma ake sayarwa a kasar ta Marroko.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: gwamnatin kasar Maroko a cikin kasa da wata guda na bayan nan sau hudu ken an tana hana buga wasu rubuce-rubucen cin mutumci da Fuska kan abubuwa masu kima da daraja na addinin musulunci da wata jaridar kasar Faransa ta buga da kuma ake sayarwa a kasar ta Marroko. Ma'aikatar watsa labarai mai kula da kafafen watsa labarai a kasar ta maroko ta fitar da wata sanarwa da a cikinta ta yi bayanin cewa; a kasa da wata guda sau hudu ken an tana hana sayar da wata jarida ta kasar Faransa da ta buga labarin cin fuskan da batanci kan addinin musulunci a wani mataki da yake a fili na neman haddasa fitina da tashin hankali ne a tsakanin musulmi .Daga cikkin abubuwan da jaridar ta kumsa akwai nuna hotuna da zanan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka sai kuma a ranar sha biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a fitowarta ta ta baya bayan nan mujallar Nouvel Observateur ta zana Ubangiji da siffar mutum yana bada umarni da aka hana sayar da wannan mujalla a fadin kasar ta Marokko.A yan kwanakin nan da =shekarun baya bayan nan kamar yadda aka sha fama a tsawon tarihin musulunci makiya na kokarin cin fuskan da bakanta addinin musulunci a kokari da himmarsu ta kula makirci da haddasa fitina a tsakanin musulmi da kuma a tsakanin musulmi da sauran takwarorinsu mabiya sauna addinai a fadin duniya amma sun kasa cimma burinsu mummuna.
947303