IQNA

Taron Cika Shekara Guda Da Gabatar Da Kur'anin Da Aka Tarjama Da Harshen Rashanci

21:57 - February 06, 2012
Lambar Labari: 2269920
Bangaren kasa da kasa, a gudanar da wani taro na cika shekara guda gabatar da wani kwafin kur'ani mai tsarki aka tarjama a cikin harshen rashanci wanda wasu malami masana kur'ani a kasar suka dauki nayin tarjamawa tare da taimakon wasu cibiyoyi na addini.



Kamfanin diallancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Today cewa, a gudanar da wani taro na cika shekara guda gabatar da wani kwafin kur'ani mai tsarki aka tarjama a cikin harshen rashanci wanda wasu malami masana kur'ani a kasar suka dauki nayin tarjamawa tare da taimakon wasu cibiyoyi na addinin muslunci a cikin gida da kuma kasashen ketare, musamman ma dag akasashen musulmi.

Wani rahoton kuma na daban yana cewa wata jaridar kasar China ta kare matakin da gwamnatin kasar ta dauka na hawa kan kujerar naki kan daftarin kudirin kasashen larabawa da yammacin turai kan rikicin kasar, wanda aka kada kuri'a kansa a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.
Jaridar wadda ta fito a safiyar yau ta rubuta cewa, daftarin kudirin kasashen larabawa da yammacin turai babu adalci a cikinsa, domin kuwa ya dora alhakin abin da ke faruwa a kasar kaco kaf a kan gwamnatin Bashar Asad, tare da kawar da ido kan abin da daya bangaren ke aikatawa, inda 'yan bingida dauke da muggan makamai suke kaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula, da sunan cewa su 'yan adawa ne ko kuma sojoji da suka balle.
Jaridar ta ce saboda rashin daidaito a cikin daftarin kudirin ne gwamnatin China ta hau kujerar naki a kwamtin tsaro kan wannan daftarin kudiri. A ranar Asabar din da ta gabata ce mambobin kwamitin tsaron majlaisar dinkin duniya 15 suka kada kuri'a kan daftarin kudirin larabawa da turawa, wanda ke neman shugaba Bashar Asad da ya safka daga kan karagar mulki, lamarin da kasashen Rasha da China suka yi fatali da shi.
947489

captcha