Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Info cewa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hamas a palastinu ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da matakan da haramtacciyar kasar Isra’ila take dauka na rusa wurare masu tsarki da suke cikin yankunan palastinu musamman ma a birnin Qods maim alfarma da kewayensa.
S shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
Wasu daga cikin musulmin kasar Azarbaijan da suke da masaniya kan harkar yanar gizo sun shiga cikin wasu shafuka mallakin gwamnatin kasar da take tsananin gaba da addinin musulunci suka bata su a wani mataki na mayar da martani kan matakan takurawa ga mabiya addinin muslunci.
A wani labarin kuma an bayyana cewa wannan jam’iya tan ada manufofi na siyasa da suka yi daidai da mahnarta, ta yadda take son saka addini ya zama shi ne ma’anu a cikin dukaknin lamurranta na siyasa, haka nan kuma idan ta samu karbuwa a wajen al’ummar kasar tana sa ran za ta kawo gagarumin canji.
948209