Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an bude wani shafin sadarwa na yanar gizo da ke yin bayani kan boren al'umamr kasar Bahrain da kuma yadda mahukuntan kasar suke daukar matakan murkushe boren da karfin tuwo ba tare da kasashen duniya sun ce uffan kan hakan ba sakamon dasawar da sarakunan kasar ke yi da kasashen turai.
Jaridar ta kawo labarin da ke cewa, Dubun dubatar mutanen ne suka tarbi ministan harkokin wajen Rasha a birnin Damascus, domin nuna godiyarsu da matakin da Rasha da China suka dauka na kin amincewa da daftarin kudirin kasashen larabawa da yammacin turai a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, da ke neman shugaba Asad ya safka.
Rasha da China dai sun ki amincewa da wannan daftrain kudiri ne saboda abin da suka kira rashin adalci a cikinsa, domin kuwa ya dora dukkanin abin da ke faruwa a Syria kan gwamnati, tare da kauda kai kan ayyukan da 'yan ta'adda ke aikatawa da sunan adawa, ta hanyar tayar da bama-bamai da bude wuta kan mai uwa da wabi ko sace mutane da abin da ya yi kama da haka.
A ganawar da ta gudana tsakanin shugaba Bashar Asad da kuma ministan harkokin wajen Rasha Sargie Lavrov, shugaba Asad ya jaddada cewa kofar tattaunawa bude take a kowane lokaci ga dukaknin bangarorin siyasar kasar, daga ciki kuwa har da wadanda suka dauki makamai suka bude fagen daga tsakaninsu da dakarun gwamnati. A nasa bangaren ministan na Rasha ya ce kasarsa za ta taimaka domin ganin an kawo karshen rikicin da kasar Syria take fama das hi. 948627