IQNA

Malaman Addini A Indiya Sun Jinjina Hadin Kan Musulmin Duniya

Bangaren siyasa da zamantakewa; malamai mabiya mazhabobin shi'a da sunna a kasar Indiya a wani zama na hadin guiwa da suka gabatar a daidai lokaci na tunanawa da irin ranar da aka haifi ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka sun jinjina hadin kai da zama tsintsiya daya a tsakanin musulmin duniya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Irn ne ya watsa rahoton cewa; malamai mabiya mazhabobin shi'a da sunna a kasar Indiya a wani zama na hadin guiwa da suka gabatar a daidai lokaci na tunanawa da irin ranar da aka haifi ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka sun jinjina hadin kai da zama tsintsiya daya a tsakanin musulmin duniya.Malaman addinin musulunci da ya hada bangarorin yan shi'a da kuma nay an sunna a ranar sha shidda ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya suka gudanar da wannan zama da taro a tsakaninsu inda aka samu halartar hujjatul Islam Mahdawi pur wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Indiya da kuma mukarrabansa da wani adadi na malamai da kuma musulmi masu yawa da suka halarci wannan taro .Kuma malamai da musulmi a kasar ta Indiya sun yi kira da babbar murya ga sauarn takwarorinsu na duniya das u hada kansu da magance matsalolin da bas u taka kara sun karya bad a kuma samar da yanayi na kusantar juna domin yin haka shi ne mafi alheri a tsakaninsu das u da shugabanninsu a maimakon su samu rabuwar hankali da ci gaba da sabani a tsakanin musulmin duniya da hakan ke amfanar da makiyansu da a kullum a tsawon tarihi suke kula makircin rarraba kawunan musulmi da shugabanninsu.

948756