IQNA

Bincike A Kasar Tailand Kan Mahangar Musulunci Dangane Da Iyalai

Bangaren siyasa da zamantakewa; a kasar Tailand ana gudanar da wani taron bincike kan mahangar addinin Musulunci dangane da iyali da kuma aure da matsayinsa a rayuwar zamantakewa kuma ana gudanar da wannan taro ne a Otel din Regent Bangkok .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Irn ne ya watsa rahoton cewa; a kasar Tailand ana gudanar da wani taron bincike kan mahangar addinin Musulunci dangane da iyali da kuma aure da matsayinsa a rayuwar zamantakewa kuma ana gudanar da wannan taro ne a Otel din Regent Bangkok. A ranar sha shidda ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne daga karfe takwas na safe zuwa karfe hudu na marece agogon kasar aka gudanar da wannan taro na binciken mahanga da muhimmancin gina iyalai da matsayin aure a mahangare addinin musulunci .Kuma an samu halkartar musulmi da masu iyali da ma'aurata da suka samu dammar halartar wannan taron bincike kuma wasu da dama daka cikin da aka yi hita das u dangane da wannan taron sun bayyana gamsuwa da jin dadinsu da jawabai da bincike da kuma baja=hasi na ilimi da tarihi da aka gabatar a gurin wannan taro da kuma yadda aka fayyace masu mahangar musulunci kan wannan abubuwa masu matukar muhimmanci a rayuwar dan adam a tsawon tarihi.

948863