Bangaren siyasa: komandan sojojin ruwa na rundunar sa kai ta kare juyin juya halin musulunci a Iran a wata ganawa day a yi da komandan sojojin ruwar kasar Oman ya bayyana cewa: Amerika tana kokarin cusa da yaudarar wasu kasashen larabawa su shiga cikin mummunar siyasarta da burin cimma mummunar siyasarta na mamaye yankin da haddasa sabani a tsakani.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Irn ne ya watsa rahoton cewa; komandan sojojin ruwa na rundunar sa kai ta kare juyin juya halin musulunci a Iran a wata ganawa day a yi da komandan sojojin ruwar kasar Oman ya bayyana cewa: Amerika tana kokarin cusa da yaudarar wasu kasashen larabawa su shiga cikin mummunar siyasarta da burin cimma mummunar siyasarta na mamaye yankin da haddasa sabani a tsakani.Ali Fadawi komandan sojojin ruwa na rundunar sa kai ta kare juyin juya halin musulunci a wannan ganawa ya yi bayani dalla dalla kan bakar siyasar Amerika da kuma mummunan burin da take son cimmawa a wannan yankin inda ya jaddada cewa a yau ana bukatar hadin kai a tsakanin kasashen yankin domin kare kansu da kula killawa da hana tasirin makircin Amerika na haddasa rikici da fadada bakar siyasarta a yanki.Sai dai ya kara da cewa ana bukatar wayewa da fahimta ta gari da aiki da hankali a tsakanin gwamnatoci da al'ummomin yankin kafin daukan duk wani mataki da kuma tunkarar wannan lamari na kokarin cinna wutar fitina a yankin gabas ta tsakiya.
949421