IQNA

Taron Kasa Da Kasa Ta Tattaunawar Addinai a Kozovo

11:05 - February 09, 2012
Lambar Labari: 2271671
Bangaren nazari da ilimi: taron kasa da kasa ta tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai da za a yi a watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jamirae Amerika da ke jamhuriyar Kozovo.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa ta tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai da za a yi a watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jamirae Amerika da ke jamhuriyar Kozovo. Christopher Hall shugaban jami'ar ta Amerika a kasar Kozovo ne a wata ganawa day a yi da Na'im Tarnava babban mai bayar da fatawa a kasar Ta Kozovo a darul Iftitah na musulmin kasar ya bada labarin gudanar da wani taron kasa da kasa ta tattauanwa da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai na duniya a wani kokarin kara kusanci da fahimtar juna a tsakanin addinai day a hada addinin musulunci,addinin kiristanci da kuma addinin yahudanci da sauran addinai. Irin wannan taro na kasa da kasa da zai hada mabiya addinai daban daban na duniya ko shakka babu zai taimaka matuka gaya wajan samar da hadin kai da kara kusanci a tsakaninsu da kuma samar da hadin kai da sulhu a duniya baki daya.

949703

captcha