IQNA

Bude Zaman Taron Makon Hadin Kai A Birnin Tehran

A jiya laraba ne aka bude babban zaman taron makon hadin kai na kasa da kasa karo na ashirin da biyar a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, zaman da ya samu halattar manyan baki daga sassa daban daban na duniya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Zaman babban taron makon hadin kai na kasa da kasa karo na ashirin da biyar a wannan shekara ya samu halattar manyan jami'an gwamnatocin kasashe, manyan malaman addinin Musulunci da kuma masana da manazarta da suka fito daga kasashe 57 na duniya, kuma mabiya mazhabobin Musulunci daban daban.

Babban sakataren cibiyar kasa da kasa domin samar da hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci Ayatullahi Sheikh Muhammad Ali Taskhiri ne ya bude zaman taron, inda a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Hakika an samu haihuwar sabon yankin gabas ta tsakiya ta hanyar da ta yi hannun riga da bakar manufar siyasar gwamnatin Amurka da albarkar bullar fadakar Musulunci a yankin.

Sheikh Maulawi Muhammad Is'hak Madani Shugaban Majalisar Kolin Cibiyar kasa da kasa domin samar da hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci a nashi jawabin ya furta cewa: Lalle fadakar Musulunci da ta kunno kai a wannan zamani ta samo asali ne sakamakon zubar da jinin dubban shahidai a kasashen musulmi, kuma wajibi ne a kan al'umma sun jure duk wata wahala, matsin lamba da takunkumi domin cimma manufar wannan yunkuri na fadakar Musulunci a kasashensu.

A jawabinsa ga zaman babban taron kasa da kasa domin samar da hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci karo na ashirin da biyar; Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Labanon Nabih Berri wanda Kamal Khalil Hajj Hamdan ya gabatar a madadinsa ya bayyana cewa: Tabbas nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ta zame wata babbar cibiyar wayar da kai a dukkanin bangarorin rayuwa da a halin yanzu ake ganin tasirinta a dukkanin kasashen musulmi. Khalil ya kara da cewa: Hakika samun hadin kai tsakanin al'ummar musulmi shi ne babban wajibin da ke gabanmu, kuma shi ne sharadin farko na ci gaba da wanzuwar wannan fadakar Musulunci da ta kunno kai, tare da kare ta daga sharrin makiya.

Har ila yau Khalil ya bayyana cewa: A halin yanzu al'ummar musulmi suna fuskantar barazana da kalubale musamman ganin yadda yahudawan sahayoniyya ke kokarin rusa wajaje masu tsarki na musulmi misalin masallacin Qudus, haramin Ibrahimi da ci gaba da aiwatar da kisan gilla kan al'ummar Palasdinu.

A nashi jawabin Muftin kasar Siriya Sheikh Badruddeen Hasun ya fara ne da jinjinawa shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadin Najad da cewa: Hakika babban abin alfahari ne gare ni ganin shugaban kasar Iran ya fara gabatar da jawabinsa a gaban mumbarin Majalisar Dinkin Duniya da salati ga manzon Allah da iyalan gidansa, kuma yana magana da duniya da kalmar addinin Musulunci wanda da ita ce Allah ya daukaka mu.

Sheikh Hasun ya kuma bayyana cewa: Hakika mu al'ummar musulmi al'umma guda ne kafin kasancewarmu 'yan shi'a ko 'yan sunna, kuma duk wata mahangarmu tana bayan mahangar annabinmu ne da na jikansa Ja'afar Sadiq, don haka wannan shi ne tushen hadin kai.

Manufar gudanar da zaman taron kasa da kasa kan hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci ita ce shimfida matakan samar da hadin kai da taimakekkeniya tsakanin al'ummar musulmi da irin rawar da malamai zasu taka a fagen samar da kusancin ra'ayi a fannonin ilimi musamman a bangaren ilimin fikihu, usulu, akida, tafsirin alkur'ani da sauransu, kamar yadda zaman taron ke tattauna al'amuran kasashen musulmi da matsalolin da ke addabar musulmi da neman hanyar warware su.

949912