Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO cewa, shugaban kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu Abdulazizi Tuwaijari ya bayyana cewa, batun hadin kai tsakanin dukaknin al’ummar musulmi wajibi ne a cikin addinin muslunci, kuma rarrabar kai tsakaninsu harm ne a cikin wannan addini mai girma saboda haka dole a kn musulmi idan suna son rayuwa cikin daukaka da karama su hada kansu ba tare da bat alokaci ba.
A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yunkurin al'ummomin kasashen musulmi na kifar da shugabannin kama-karya ‘yan amshin shatan manyan kasashen duniya a matsayin lamari mai matukar muhimmanci sannan kuma wani mafari na yunkurin ganin bayan lalatattun cibiyoyin yahudawan sahyoniya da ma'abota girman kan duniya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sakamakon wannan yunkuri mai cike da albarka, da yardar Allah al'ummar musulmi za su sake dawo da daukaka, ‘yanci da kuma tsayin dakan da suke shi a baya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana matasan kasashen musulmin a matsayin masu dauke da babbar bishara ga makomar al'ummar musulmi, daga nan sai ya ce: Farkawar da matasan kasashen musulmi suka yi, lamari ne da ke kara irin fatan da ake da shi na farkawar dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu tarihin bil'adama yana fuskantar wani gagarumin sauyi mai girma ne, daga nan sai ya ce: Bil'adama dai sun gwada dukkanin akidu na abin duniya da suka hada da gurguzu, jari hujja, ‘yan kasanci da rashin yarda da Ubangiji, to amma a halin yanzu suna a wani sabon yanayi ne wanda babbar alamar hakan ita ce irin yadda al'ummomi suka koma ga Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimako daga wajen karfi maras karewa na Ubangiji da kuma dogaro da koyarwar Ubangiji.
951087