IQNA

An Bayar Da Wata Lambar Yabo Ga Shugaban Musulmin Kasar faransa

20:05 - February 11, 2012
Lambar Labari: 2272290
Bangaren kasa da kasa, an bayar da wata lambar yabo ta musamman shugaban majalisar musulmin kasar Faransa a matsayin mutumin da ya taka gagarumar rawa wajen ya hada kan mutane da girmama juna mai makon nuna kyama da banbancin addini ko wariyar fata da abin da ya yi kama da haka daga cikin matsalolin mutanen kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Atlainfo cewa, an bayar da wata lambar yabo ta musamman shugaban majalisar musulmin kasar Faransa a matsayin mutumin da ya taka gagarumar rawa wajen ya hada kan mutane da girmama juna mai makon nuna kyama da banbancin addini ko wariyar fata da abin da ya yi kama da haka daga cikin matsalolin mutanen kasar, musamman ma musulmi da ake cutarwa fiye da kowa a kasar saboda addininsu.
A wani labarin kuma ana shirin gudanar da wani zaman taro a birnin Lyon na kasar Faransa mai taken addinin muslunci da sabbin ilmomi wanda kwamitin babban masallacin birnin zai dauki nauyin shiraya da gudarwa kamar dai yadda ya saba daukar nauyin shirya taruka irin wadannan a garuruwa daban-daban.
Babban masallacin birnin lyon dai na daga cikin muhimamn cibiyoyin addi8nin muslunci a cikin kasashen nahiyar turai, wanda yake gabatar da shirye-shirye na fadakarwa ga mabiya addinin muslunci mazaun akasar, haka nan kuma ya kan shiya taruka domin nuna ma ‘yan kasar da ba mabiya addinin muslunci matsayin addini kan lamurra da dama da suka danganci rayuwa mutum.
Gudanar da wani zaman taro a birnin Lyon na kasar Faransa mai taken addinin muslunci da sabbin ilmomi wanda kwamitin babban masallacin birnin zai dauki nauyin shiraya da gudarwa na da matukar muhimmanci gaske ga bangaren yada manufofin addini a kasar.
951060


captcha