IQNA

An Kirayi Musulmin Switzerland Da Suka Wata Majalisa Ta Musulmin Kasar

20:04 - February 11, 2012
Lambar Labari: 2272292
Bangaren kasa da kasa, babbar majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland ad suka kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na safir news cewa, babbar majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland ad suka kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu da abin da ke kai da komowa dangane da su, musamman am acikin yanayi da musulmin kasar suke fuskantar barazana.
Babban kwamitin musulmin nahiyar turai ne ya yi wannan kira, bisa la’akari da cewa a halin yanzu gwamnatocin kasashen turai suna daukar matakai na takura musulmi ta hanyoyi da dama, wanda hakan ya sanya ala tilas musulmi duk inda suke a cikin kasashen nahiyar su mike domin kare hakkokinsu, musamman kasashe da musulmi suke da yawa kamar Switzerland Jamus da kuma Faransa gami da Birtaniya.
Majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland da su kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu a dukaknin buiranan kasar, domin warware matsalolinsu.
951130

captcha