Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, ana shirin gudanar da wani taro na tunawa da wadanda suka yi shahada a tafarkin gwagwarmaya a karkashin inuwar kungiyar hizbullah a kasar Lebanon a fafatawar da suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin ‘yan shekarun nan.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu na Lebanon da Libya kamar dai yadda majiyoyi daga dukaknin bangarorin biyu suka mabata.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali, mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar.
951670