Bangaren kasa da kasa: a yau al'ummar musulmi na fuskantar wani irin yaki da makirci da yafi yakin kai hari da sojoji da makamai muni domin a yau ana kai masu harin yaki ne kan al'adu,zamantakewa da karya masu karfin tattalin arziki kuma wannan shi ne abin da musulmi ke fuskanta a yau.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a yau al'ummar musulmi na fuskantar wani irin yaki da makirci da yafi yakin kai hari da sojoji da makamai muni domin a yau ana kai masu harin yaki ne kan al'adu,zamantakewa da karya masu karfin tattalin arziki kuma wannan shi ne abin da musulmi ke fuskanta a yau. Sheikh Na'im Kasim mukaddashin babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ya gabatar da wani jawabi a lokacin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma a harda a kasar labanon a ranar ashirin da uku ga watan Bahamn na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bayyana cewa; a yau al'ummar musulmi na fuskantar babban yaki da yafi yakin kai masu hare hare da makamai mufi domin a yau wani nau'in yaki ne na gurbata masu al'adu ,zamantakewa da kuma tattalin arziki. Kuma a yau ya kamata musulmi su hada kansu domin fuskantar wannan matsala tun kafin guri ya kurace masu da yi masu sakiyar da babu ruwa a kusa.
952231