IQNA

Al'ummar Palasdinu Na Bukatar A Taimaka Mata

18:30 - February 14, 2012
Lambar Labari: 2274260
Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khaminaee, ya kara jadda matsayin J.M.I na goyon baya ga al-ummar kasar Palasdinu har zuwa lokacinda za'a 'yentar da dukkan kasar Palasdinu daga ikon yan mamaya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa:
Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khaminaee, ya kara jadda matsayin J.M.I na goyon baya ga al-ummar kasar Palasdinu har zuwa lokacinda za'a 'yentar da dukkan kasar Palasdinu daga ikon yan mamaya.
Jagoran ya bayyana haka ne a ganawarsa da Priministan kasar ta Palasdinu Isma'ila Haniyya wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran tun ranar jumma'a.
Jagoran ya bukaci shuwagabannin kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Palasdinu da kada su bar masu ra'ayin sulhutawa da HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA su sulale su shiga tsakaninsu.
A nashi bangaren Isma'il Haniyya ya gabatar da godiyarsa ga al-umma da kuma gwamnatin kasar Iran kan goyon bayan da suke bawa al-ummar Palasdinu ta banagarori da daban daban.
Priministan ya kara jaddada manufofin kungiyarsa ta Hamsa na 'yentarda dukkan kasar palasdinu, rashin amicewa da dukkan tattaunawa da haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma dogewa kan gwagwarmaya da H.K.L. kan tafarkin addinin Musulunci.

952045
captcha