IQNA

Taron Manema Labarai Tsakanin Ahmadi Najad Da Isma'il Haniya

18:30 - February 14, 2012
Lambar Labari: 2274261
Shugaban kasar Iran Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce Iran za ta ci gaba da taimaka wa al'ummar Palasdinu zai zuwa lokacin da suka 'yanto kasarsu ta asali daga mamayar Yahudawan Sahyuniyya.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa:

Shugaban kasar Iran Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce Iran za ta ci gaba da taimaka wa al'ummar Palasdinu zai zuwa lokacin da suka 'yanto kasarsu ta asali daga mamayar Yahudawan Sahyuniyya.
Ahmadinejah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da zababben firayi ministan Palasdinu Isma'il Haniyyah wanda yake gudanar da ziyara a nan Iran, inda ya ce Iran tana daukar wanzuwar Haramtacciyar Kasar Isra'ila a matsayin barazana ga al'ummar Palasdinu da kuma musulmin duniya, saboda haka a cewar shugaban na Iran, gwagwarmaya da kuma tsayuwa tsayin daka su ne kawai za su kai ga 'yantar da Palsdinu a irin wannan yanayi.
Shi ma dai Firayi ministan na Palasdinu, ya jinjina wa al'ummar Iran a game da irin gwagwarmayar da suka gudanar domin dora kasar a kan tsari na Islama, sannan kuma ya bayyana Iran a matsayin wacce take sahun gaba wajen taimaka wa Palasdinawa domin 'yantar da su daga mamaya yahudawan Sahyuniyya.


952288
captcha