IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Yi Allawadai Da Watsa Hotunan Cin Zarafin Manzo A Faransa

18:32 - February 15, 2012
Lambar Labari: 2275009
Bnagaren kas ada kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun muslunci ta ISESCO ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da wata wasu hotuna na cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun muslunci ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da wata wasu hotuna na cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da wasu marassa kunya da ke neman tashin hankali a kasar Faransa suka yi.
A bangare guda kuma babbar majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland ad suka kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu da abin da ke kai da komowa dangane da su, musamman am acikin yanayi da musulmin kasar suke fuskantar barazana.
Babban kwamitin musulmin nahiyar turai ne ya yi wannan kira, bisa la’akari da cewa a halin yanzu gwamnatocin kasashen turai suna daukar matakai na takura musulmi ta hanyoyi da dama, wanda hakan ya sanya ala tilas musulmi duk inda suke a cikin kasashen nahiyar su mike domin kare hakkokinsu, musamman kasashe da musulmi suke da yawa kamar Switzerland Jamus da kuma Faransa gami da Birtaniya.
Majalisar mabiya addinin muslunci da ke nahiyar turai ta kiray mabiya addinin muslunci da suke cikin kasar Switzerland da su kafa wata babbar majalisar ta musulmin kasar, wadda za ta rika bin kadun hakkokinsu da kuma sanin dukaknin lamurransu a dukaknin buiranan kasar, domin warware matsalolinsu. 953006
captcha