IQNA

Komawa Dandalin Shahidai Shi ne Abin Da Masu Bore Suka Yi Rantsuwa kansa

18:33 - February 15, 2012
Lambar Labari: 2275011
Bnagaren kasa da kasa, masu gudanar da zanga-zangar lumana sun dauki alkawalin komawa dandalin Lu’alua da aka fi sani da dandalin shahidai tun bayan fara gwagwarmayar kawo karshen mulkin kama karya akasar Bahrain duk kuwa da matakan rashin iamni da sarkin kasar ke dauka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masu gudanar da zanga-zangar lumana sun dauki alkawalin komawa dandalin Lu’alua da aka fi sani da dandalin shahidai tun bayan fara gwagwarmayar kawo karshen mulkin kama karya akasar Bahrain duk kuwa da matakan rashin iamni da sarkin kasar ke dauka na murkushe duk wani yunkuri.
Mutanen kasar Bahrain za su ci gaba da yunkurin na neman sauyi a cikin harkokin mulki da siyasar kasar ta hanyar lumana har sai sun cimma wannan buri nasu ba tare da ja da baya ba kamar yadda kakakin jam’iya Wifaq mai adawa ya fada a cikin wani bayani a yau.
A bangare guda kuma kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta kirayi mahukuntan kasar Bahrain da su yi bayani kan azabtar da mutane da ake yi a cikin gidajen kurkukun kasar sakamakon shiga zanga-zangar neman sauyi.
A cikin bayanin da kungiyar ta fitar, ta tabbatar da cewa ana gana wa mutane masu tarin yawa azaba a cikin gidajen kurkukun masarautar Bahrain, laifinsu kuwa shi ne sun shiga zanga-zanga neman sauyi a cikin harkokin mulkin kasar, tare da neman hakkokinsu na 'yan kasa da aka haramta musu. Bayanin ya ce jami'an tsaron Bahrain sun kame wata matashiya mai suna Fadila Mubarak saboda tana sauraren wakokin neman sauyi a cikin motarta, kuma an azabtar da ita, daga bisani kuma kotu ta daure watanni 18 saboda wannan zargi.
Tun bayan fara gudanar da zanga-zanga neman sauyi a kasar Bahrain ta hanyar lumana a cikin Fabrairun shekarar da ta gabata, ya zuwa yanzu mutane da daman e suka rasa rayukansu, wasu kuma suka samu raunuka, wasu kuma ake tsare da su a gidajen kurku, amma duk da hakan al'ummar kasar ba su canja salon zanga-zangar su ba.

953014



captcha