Bangaren al'adu da fasaha: a daidai wannan lokaci na murnar zagayowar shekaru talatin da uku da samin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran an fitar da wata mujalla ta musamman cikin kala a kasar Suriya kan irin nasarorin da Jamhuriyar musulunci ta Iran ta samarwa kanta da al'ummar Iran cikin daraja da daukaka kuma mujallar ta kumshi shafika dubu biyu.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a daidai wannan lokaci na murnar zagayowar shekaru talatin da uku da samin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran an fitar da wata mujalla ta musamman cikin kala a kasar Suriya kan irin nasarorin da Jamhuriyar musulunci ta Iran ta samarwa kanta da al'ummar Iran cikin daraja da daukaka kuma mujallar ta kumshi shafika dubu biyu.A cikin wannan mujallar mai shafuka dubu biyu an kawo labarai daban daban masu kayatarwa da kuma masu ban sha'awa da aka jero irin nasarorin da jamhuriyar musulunci ta Iran ta samar a tsawon shekaru talatin da uku da samin nasarar juyin juya halin musulun a Iran .Har ila yau an yi bayani da fadakarwa kan yadda ya kamata sauran kasashen musulmi da al'ummomin musulmi ya kamata su yi koyi da wannan tsari na jamhuriyar musulunci ta Iran domin samin yanci da ci gaba ta dukan bangarori kama daga tattalin arziki,zamantakewa,akida da kuma al'adu da daidai sauransu kamar yadda sauran kasashen da suka ci gaba suka samin yanci da ci gaban da suke takama da shi.
953436