IQNA

Rawar Da Imam Khomeini ® Ya Taka Wajan Raya Abubuwan ma'anawiya A Karkizistan

17:48 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275342
Bangaren al'adu da fasaha: rawar da Imam Khomeini ® ya tara wajan raya abubuwa na addini da tunani na ma'anawiya a kasar karkizistan kuma a ranar ashirin da biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dalilin tunawa da zagayowar cika shekaru talatin da biyar da nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a wani taro da aka gudanar a garin Bishkuk fadar mulkin kasar ta Karkizistan aka yi bincike kan rawar da imam Khomeini ya taka a wannan kasa.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: rawar da Imam Khomeini ® ya tara wajan raya abubuwa na addini da tunani na ma'anawiya a kasar karkizistan kuma a ranar ashirin da biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dalilin tunawa da zagayowar cika shekaru talatin da biyar da nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a wani taro da aka gudanar a garin Bishkuk fadar mulkin kasar ta Karkizistan aka yi bincike kan rawar da imam Khomeini ya taka a wannan kasa.A wannan taro na bincike irin gudummuwa da rawar da imam Khomeini ® muassassin juyin juya halin musulunci a Iran ta yi a wannan kasa ta Karkazistan masana da marubuta da malamai da masu kula da harkokin al'adu a wannan kasa sun yi dogon bincike da nazari kan irin jan aiki da gudummwar da Imam Khomeini ya bayar wajan ciyar da wannan bangare na addini da abubuwa na ma'anawiya da kuma dogaro da kai day a samar a tsakanin al'ummomi daban daban na wannan kasa da zama a bin koyi a tsakanin masana da marubuta da kuma uwa uba malaman addini a wannan kasa.
953441
captcha