IQNA

Gidan Sarautar Khalifa Ya Zabi Bin Tafarkin Mulkin Kama Karya

18:07 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275354
Bangaren kasa da kasa, bababr jam'iyar siyasa mai adawa akasar Bahrain ta Alwifaq ta sanar cewa didan sarautar Khalifa ya zabi bin tafarki na salon mulkin kama karya a kan al'ummar kasar masu neman hakkokinsu da aka haramta musu tsawon shekaru.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na jaridar al-safir ta kasar Lebanon cewa, bababr jam'iyar siyasa mai adawa akasar Bahrain ta Alwifaq ta sanar cewa didan sarautar Khalifa ya zabi bin tafarki na salon mulkin kama karya a kan al'ummar kasar masu neman hakkokinsu da aka haramta musu tsawon shekaru duk kuwa da irin boren da suke fuskanta kan haka daga al'ummar kasar.
Jamiyar wadda take da goyon baya na mafi al'ummar kasar ta fitar da bayanai na yin Allawadai da wannan salon mulki na fir'aunanci da sarakunan Bahrain suke dauka da ke cewa, a wannan lokacin muna ganin yadda a cikin Masar da sauran kasashe su ke kokarin haddasa sabani da kuma fadace-fadace. Kuma shakka babu za su kai ga haddasa fitina da dasa bama-bamai."
Bugu da kari jagoran ya yi ishara da hanyoyin da za a yi aiki da su domin kalubalantar makirce-makircen yammacin turai inda ya ce: "Al'umma suna son kare mutuncinsu ne da kuma daukakarsu. Mutunci da daukaka wadanda su ke a matsayin ginshikin kiran da manzon Allah ya zo da shi. A duk lokacin da al'umma ta zama wacce ta ke son riko da musulunci to kuwa za ta kasance mai son kare mutuncinta da daukakarta. Ma'ana ita ce cewa riko da musulunci yana nufin magance makarkashiyar da makiya su ke kitsawa.
953727


captcha