IQNA

Muftin Kudus Ya Yi Allah wadai Da Hana Kiran Salla A Nablus

Bangaren kasa da kasa; babban mai bayar da fatawa a Kudus da Palasdinu ya fitar da wata sanarwa da bayanin da a cikin yake yin Allah wadai da babbar murya kan matakin hana yin kiran salla a masallacin Salman farisi da ke kauyen Burin a kudu maso gabacin Nablus da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ta yi da cewa wannan wani zalunci da wuce gonad a iri ne kan musulmi.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriya musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: babban mai bayar da fatawa a Kudus da Palasdinu ya fitar da wata sanarwa da bayanin da a cikin yake yin Allah wadai da babbar murya kan matakin hana yin kiran salla a masallacin Salman farisi da ke kauyen Burin a kudu maso gabacin Nablus da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ta yi da cewa wannan wani zalunci da wuce gonad a iri ne kan musulmi.Sheikh Muhammad Husein babban mai bayar da fatawa a kudus da palasdinu a ranar ashirin da biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan wannan mataki da mahukumtan a gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka na hana yin kiran salla da kuma yake kiran musulmin duniya das u tashi tsaye domin tunkarar wannan gasa aya a hannu da gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila ke yi wa musulmi da kuma kawo karshen wannan halin takaici da zalunci da gwamnati da mahukumta a Haramtacciyar kasar Isra'ila ke nunuwa musulmin Palsdinu da hana su yin addininsu na musulunci a yankinsu.
954270