Bangaren fikira da ilimi, za a gudanar da wani zaman taro mai taken matsayin mata a mahanagar addinin muslunci da kuma hakkokinsu wanda zai gudana abirnin Gurozni fadar mulkin jamhuriyar Chehcniya tare da halartar masana da kuma malaman addinin muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro mai taken matsayin mata a mahanagar addinin muslunci da kuma hakkokinsu wanda zai gudana abirnin Gurozni fadar mulkin jamhuriyar Chehcniya tare da halartar masana da kuma malaman addinin muslunci, da kuma malaman jami’oi da aka gayyata daga wasu sassa na kasar.
A wani bangare kuma iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Asia One cewa, an fara gudanar da wani taron bayar da horo ga sojojin kasar Burnei kan karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda ta yadda hakan zai ba su damar sanin hanyoyon karfafa karatu da harda littafin mai tsarki kamar dai yadda aka saba yi a kasar.
Burnei na daga cikin kasashen musulmi da suke bayar da matykar muhimamnci ga lamurra da suka danganci a ddinin muslunci a cikin dukaknin harkokin kasar, da suka hada da na gwamnati na jama’a daidauiku, da hakan ya hada lamurran soji na tsaro a kasar ta Burnei.
Gudanar da wani taron bayar da horo ga sojojin kasar Burnei kan karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda ta yadda hakan zai ba su damar sanin hanyoyon karfafa karatu da harda littafin mai tsarki yana da matukar amfani ga rundunar soji ta kasar musulmi, domin ko ba komai hakan zai ba su damar yin aikinsu bisa koyarwar addininsu.
955376