Bangaren fikira, Malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza, ya bayyana Irfani da cewa hanyoyi na farfaganda na daga cikin mahyoyin da ayin amfani da su wajen watsa gurbatacciyar akida a tsakanin mutane cikin sauri da hakan ya hada da mahanga ta masu raya bin sahihin tafarkin irfani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza, ya bayyana Irfani da cewa hanyoyi na farfaganda na daga cikin mahyoyin da ayin amfani da su wajen watsa gurbatacciyar akida a tsakanin mutane cikin sauri da hakan ya hada da mahanga ta masu raya bin sahihin tafarkin irfani a cikin kasashen musulmi.
Dangane da ziyartar kabruka da muka yi a baya, ana ziyartar wadannan kabaruruka da ma wasun su daga bangaren jama'a saliha, wadanda suke zaune a kusa da waurin, kuma sukan taru a wurin a wasu darare da ranaku na musamman, haka nan ma wasu jama'a da dama sukan kawo musu ziyara daga wuri mai nisa, har ma daga wasu kasashen duniya daban-daban. Don haka muna iya cewar ana yawan ziyartar kabarurukan A'immar daga iyalan gidan manzo a kowanne lokaci, amma an fi cukowa a mako- mako, wato idan har ma bai zama kullum ba kenan ga wadanda suke kusa da kabarin.
Babu wani haddi ko iyaka ta fuskacin lokaci ko kuma wani lokacin na musamamn game da ziyarar kabrurukan manzo da iyalan gidansa tsarkaka, amma dai duk da haka a kwai wasu lokuta kebantattu da a kafi ba su muhimmanci kuma aka fi taruwa a cikinsu, kuma wannan na faruwa ne kodai saboda wani fifiko da daraja.
Akwai wasu kalamai tsakanin masana masu bincike game da batun wurin da kabarin sayyida Zainab ‘yar Imam Aliyu bin Abi Talib (as) take inda wasu sashi daga cikinsu suka tafi kan cewar kabarinta yana Gauda ne da ke birnin Damaskas da ke kasar Syria, wasunsu kuma suka tafi a kan cewar kabarinta yana birnin Alkahira na kasar Masar ne, wasu kuma suka bi wata maganar daban, sai dai wadannan kalamai su ne suka fi shahara kuma suka fi zama sanannu a tsakankanin mabiya Ahlul baiti (As) da ma masoyansu da sauran al'ummar muslumai baki daya. Har ila yau akwai wani hadisi daban game da batun kabarin kan Imam Hussaini (as) inda wasu suka ce an bizne kansa ne a birnin Damaskas na kasar Syria, wani ra'ayin kuma ya ce an bizne kan nasa ne a birnin Alkahira, sai dai wanda aka sani a wurin mabiya ahlul bait shi ne an bizne kansa a birnin karbala ne tare da sauran jikinsa mai tsarki yardar Allah ta tabata gare shi amin. Lokacin da sauran iyalan gidansa da aka kama a matsayin ribatattun yaki suka dawo daga wurin Yazid dan Mu'awiya.
Don haka ranakun da suke da alaka da ranakun haihuwa ko kuma wafati (rasuwa) ko shahadar wani daga cikin Iyalan gidan manzo ko yayansu, ana so a bada kulawa ta musamman wajen ziyarar wannan Imamin ko kuma zuri'arsa a daidai wannan lokaci.
Hakazalika daren juma'a da ranarta ana bada wata kulawa ta musamman, a gefe guda saboda falallar dake tattare da ita, ko kuma saboda a cikinta ne akan bada hutu na gama gari, musamaman ma karanta ziyarar Imam Hussaini (As) a daren Juma'a, na daga cikin abin da ya zo na falala da lada da take da shi.
Haka ma ranaku masu albarka kamar ranakun idi, domin kasantuwar wadanan abubuwa biyu da suka kebanta da su, yasa ake kira zuwa ga muhimmancin karanta ziyara da kuma halartar kabarinsu a cikin su.
Bugu da kari a kan wannan za mu ga cewa hutun makarantu da ake badawa a lokacin zafi na daya daga cikin wasu dalilai da suke kara karfafa gwiwa domin kai ziyara a lokutan. Saboda a lokacin ne aka fi samun dama, kuma yafi da cewa a yi tafiye-tafiye ga iyali da kuma shakatawa, musamman ma zuwa wurare masu nisa, hakan yasa za a ga wasu kabarurkan na A'imma an fi samun cunkoson miliyoyin jama'a a wannan lokaci kamar yadda yake a hubbaran Imam Ridha (as) da hubbaran Imam Hussain da na Amirul mu'aminina (as) da ma na sayyida Zainab da ke birnin Damaskas na kasar Syria.
Kamar dai yadda muka riga muka sani a bayanan da suka gabata cewar; akwai ziyara ta musamman a wasu lokuta da aka ayyana da kuma ta bai daya da ake yin ziyara da ita a kowanne lokaci. Adadin masu ziyara yakan yi karanci idan aka kwatanta da wasu hubbarorin, saboda dalilan siyasa da wannan kasar take ciki, saboda haka ne ma muke ganin karancin masu ziyara a kasar Iraki, ba don komai ba sai saboda zaluncin gwamnatin shugaban jam'iyar ba'as na kasar, da ya haramata wa masu ziyara zuwa wajen, ko kuma ya kuntata musu da ma sauran mutane baki daya. Haka ma a bin da ke faruwa a kasar Iran, sakamakon kallafaffen yakin zalunci da kuma takunkumin da aka kakaba wa jamhuriyar muslunci ta Iran, daga bangaren wasu gwamnatocin kasashe da akwai mabiya Ahlul baiti a cikinsu, amma duk da haka za a ga adadin masu ziyarar yana karuwa ne idan muka kau da ido kan wasu abubuwan, kamar yadda ake bada labarin a 'yan kwanakin nan cewar kimanin mutane miliyan biyar ne suka taru a lokacin ziyaratu Arba'in na Imam Hussain (AS) yayin da wasu miliyan uku kuma suka taru a lokacin ziyarar Ghadir a shekarar bara, to ina idan ka kwatanta da ziyarar Imam Ridha (As) a lokutan da ake wasu bukukuwa ma adadin mutane yakan kai miliyoyi masu yawa ga kowanne Imami, to akwai kari a kan wannan ziyarori na musamman ga kowanne Imami, wato (ziyarar a’imma ) ke nan da ake mata lakabi da ziyarar (jami'a) da ake ziyarar dukkan limaman gidan manzo da ita, kuma a dukkan hubbarensu da ma na zuri'arsu ba tare da wani banbanci ba, kuma wannan ziyarar tana kunshe da ma'anonin masu kayatarwa ta fuskar ma'anonita, da ma yadda aka tsara luggarta, da kuma abin da ta kunsa madaukaka. Kila abin da yafi shahara a wannan ziyara ta jami'a yana kunshe a cikin wannan ziyarori.
925989