Bangaren kasa da kasa: A ranar ashirin da takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani taro na musamman da aka samu halartar Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka bude wannan gidan tarihi na musulmi a kasar Austriya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarkin a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; A ranar ashirin da takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani taro na musamman da aka samu halartar Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka bude wannan gidan tarihi na musulmi a kasar Austriya.A garin Maburn ne aka gudanar da gagaramin wannan buki inda muslmi masu yawan gaske da wakilan gwamnatin yankin suka halarta musamman gwamnan jahar da kuma Ahmad Fahur shugaban komitin kula da dangantaka ta musulunci a kasar ta Austriya. Wannan cibiya ko shakka babu za ta taimaka matuka gaya wajan sauwake bincike da nazari da suka shafi addinin musulunci a wannan kasa da kuma bincike na tarihin addinin musulunci da sauran bangarori da suka shafi addinin .Ihsan Uglo a cikin jawabin day a gabatar yayi nuni da tasirin da gudummuwar da addinin musulunci ya yi a cikin al'ummomi daban daban da kuma fasawa da arzikin al'adu da ke kumshea cikin addinin musulunci.
955640