Bangaren kasa da kasa: Isma'il Haniya shugaban zabebbiyar gwamnati kuma firaminista a palasdinu da yankin zirin Gaza ya bayyana cewa; muna goyan baya da kasancewa tare da Adnan Khidr fursunan Palasdinu day au kwanaki satin da biyu da yake yajin aikin kin cin abinci domin isar da sako kan halin kunci da takurawa da fursunonin Palasdinu ke ciki a gidajan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarkin a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Isma'il Haniya shugaban zabebbiyar gwamnati kuma firaminista a palasdinu da yankin zirin Gaza ya bayyana cewa; muna goyan baya da kasancewa tare da Adnan Khidr fursunan Palasdinu day au kwanaki satin da biyu da yake yajin aikin kin cin abinci domin isar da sako kan halin kunci da takurawa da fursunonin Palasdinu ke ciki a gidajan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila.A ranar ashirin da takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jawabin day a gabatar bayan sallar juma'a a masallacin Alumri da ke Gaza ya bayyana cewa: dukan Palasdinawa da kungiyoyi da bangarori daban daban na al'ummar palasdinu suna goyan bayan sako fursunonin Palasdinu kuma suna tare da goyan bayan fursunan da ke yajin kin cin abinci domin nuna fushi da bayyana wa duniya halin da yake ciki a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila dab akin hali da takurawa da suke ciki tare da fadakar da duniya da al'ummomin duniya musamman hukumomi da kungiyoyi na yankin da na kasa da kasa das u maida hankali kan halin da suke ciki. Da dama daga cikin mahukumata da wakilai na kungiyoyin gwagwarmaya a palsdinu na bayyana takaici da damuwa da halin da Fursunonin Palasdinu ke ciki a gidajan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila.
955361